Wani Kwamandan ‘Yan tawayen Syria ya koma bangaren gwamnati
Wallafawa ranar:
Wani Kwamandan ‘Yan Tawayen Syria, Captain Khalid Abdel Rahman al Zamel, tare da wasu mayan sa, sun sanar da aje makaman su, da kuma komawa bangaren gwamnati.
Yayin ganawa da manema labarai a Damascus, kwamnadan wanda yayi nadamar yadda ake cigaba da kashe fararen hula, yace ta hanyar tattaunawa ne kawai za’a samo hanyar magance rikicin kasar, amma ba anfani da makamai ba, inda ya bukaci sauran Yan Tawayen da su aje makaman su, dan komawa gida.
“Mun yi shawarar mu koma cikin dakarun Syria domin mu mara musu baya kwamitin sulhu,” Zamel ya ce a yayin day a gudanar da wani taro.
Zamel dai yana tafe tare ne da wasu tsofaffin ‘yan tawaye su goma, wadand basu ce komai ba a loakcin taron.
A cewar Zamel, ba amfani da makamai bane, ko kashe mutanen da basu ci ba su sha ba hanyar da za a shawo kan rikicin na Syria.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu