Palasdinu

Abbas ya bukaci a bawa Palasdinu matsayi irin na Isra’ila a Majalisar Dinkin Duniya

Shugaban Palasdinawa, Mahmud Abbas, ya bukaci a bawa kasar Palasdinu cikakken matsayi a Majalisar Dinkin Duniya, wanda hakan zai ba ta damar zama kasa mai cin gashin kanta kusa da kasar Isra’ila. Abbas ya gabatar da wannan bukata ce a yayin da ya ke gabatar da jawabinsa, a babban zauren taron Majalisar Dinkin Duniya wanda ake kan gudanarwa a birnin New york da ke kasar Amurka.  

Shugaban Palasdinawa, Mahmud Abbas (hagu) tare da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu
Shugaban Palasdinawa, Mahmud Abbas (hagu) tare da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu baltimorechronicle.com
Talla

Sai dai Firaminsitan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, a lokacin gabatar da nashi jawabin a taron, ya yi watsi da wannan bukata da shugaban Palasdinawan ya gabatar, inda ya kwatanta ta a matsayin maganar da za a iya gurfanar da mutum a gaban kotu.

Shugaban Palasdinawan da ya samu suka daga gwamnatin Hamaz da ke Gaza, sai dai jawabin da ya gabatar a taron, ya samar mai da karbuwa daga wadanda su ka saurari jawabin a zauren taron.

A lokacin gabatar da bukatar, Abbas ya ce “muna kyautata zaton cewa, mafi rinjayen kasashen duniya na goyon bayanmu, na ganin cewa an biya mana wannan bukata, wanda hakan zai ba da damar samun zaman lafiya.”

Ya kuma yi kira ga kwamitin tsaron, na Majalisar Dinkin Duniya, da ya fitar da wata hanya wacce za ta tilasta kawo karshen cikas din, da sasantawa tsakanin bangarorin biyu ke fuskanta na tsawon shekaru biyu.

Kasar Amurka ce dai ta tare yunkurin da kasar Palasdinu ke yi na ganin cewa ta samu cikakken mukami a zauren na Majalisar Dinkin Duniya, wanda Abbas ke kokarin ya ga ya canja.

A matsayinta na kasa mai cikakken matsayi na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Amurka na da damar da za ta cirje akan wani yunkuri da kamitin tsaron Majalisar zai yi na bawa Palasdinu damar zama kasa mai cikakken iko.

Sai dai babu kasar da za ta iya hana wani matsayi da daukacin Majalisar za ta iya dauka, inda mafi yawan kasashe 193 da ke majalisar za su bi bayan Palasdinu ne.

Kokarin sasantawa tsakanin kasashen biyu ya samu cikas a shekaru biyu da su ka gabata, inda Abbas ya ki yadda da tattaunawa a yayin da Isra’ila ke cigaba da mamaye yankin Palasdinawa domin gina matsugunan Yahudawa.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI