Faransa-Africa

Hollande ya isa birnin Kinshasa domin taron kasashen masu amfani da Faransanci

Zauren da za'a gudanar da taron kasashe masu amfani da harshen Faransanci a Congo
Zauren da za'a gudanar da taron kasashe masu amfani da harshen Faransanci a Congo REUTERS/Noor Khamis

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya isa birnin Kinshasha babban birnin kasar Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo domin halartar taron kasashe masu Magana da harshen Faranci. A ziyarar da shugaban ya kai kasar Senegal a jiya Juma’a yace yanzu lokaci ne da Faransa zata kulla kawancen gaskiya tsakaninta da kasashen Africa.

Talla

Kimanin Kasashen Afrika masu Magana da harshen Faransanci 70 ne ake sa ran za su kai ziyara birnin Kinshasha domin halartar taron na kwanaki biyu inda kasashen za su yi kokarin fito da hanyoyin magance rikicin ‘Yan tawayen Congo da Mali.

Shugaba Francois Hollande ya yi alkawalin taimakawa ga ci gaban Demokradiyya a Afrika da ke fama da magudin zabe.

Shugaban yace Faransa da kasashen Afrika za su bude wani sabon babin dangantaka ta fuskanr Difolomasiya da tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.