Colombia

‘Yan tawaye da Gwamnatin Colombia za su gana a Norway

Rundunar 'Yan Tawayen FARC a masu yaki a Colombia
Rundunar 'Yan Tawayen FARC a masu yaki a Colombia Reuters

Wakilan Gwamnatin kasar Colombia, da ‘Yan Tawayen kungiyar FARC, sun isa kasar Norway, don fara tattaunawa kan tashin hankalin da aka kwashe shekaru 50 ana yi a cikin kasar. Mai shiga tsakani a taron, Humberto de la Calle, yace duk da yake baya so ya kururuta taron, yana da fata mai kyau cewar, taron zai cim ma nasara.

Talla

Babu dai wani bayani dangane da jadawalin taron. Amma wannan ne karon Farko da Gwamnatin kasar za ta fara zaunawa a teburin sasantawa da ‘Yan tawayen a birnin Oslo kafin karo na biyu su sake tattaunawa a Cuba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI