Faransa-Syria

Faransa ta bayar da tallafin kudi ga ‘Yan tawayen Syria

Wani Sojan 'Yan tawayen Syria a yankin Hanano da ke birnin  Aleppo Arewacin Syria
Wani Sojan 'Yan tawayen Syria a yankin Hanano da ke birnin Aleppo Arewacin Syria Reuters/Zain Karam

Gwamnatin Faransa ta taimakawa ‘Yan tawayen Syria da kudi masu yaki da Bashar Assad, kamar yadda Ministan harakokin waje Laurent Fabius ya tabbatar bayan ya zargi dakarun Syria suna kai hare haren bama bamai ga fararen hula.

Talla

Rahotanni sun ce kasar Faransa tana aikawa da kudade ga ‘Yan Tawayen Syria a matsayin kudin agaji, don taimakawa fararen hula da suka makale a cikin kasar, wajen sake gina gidajen yin biredi, kwashe shara da kuma kafa rundunar ‘Yan Sanda.

Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius, ya gana da wakilan kasashe 20 da kuma ‘Yan Tawayen Syria a birnin Paris, inda ya yi musu bayani akan kudi Dala miliyan biyu da aka bai wa ‘Yan Tawayen.

A lokacin da ya ke zantawa da manema labarai game da rikicin Syria a birnin Paris, Mista Fabius yace kasashe da dama suna neman shiga tsarin taimakawa fararen hula a Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI