Amurka

Kazamar Guguwa ta yi barna a Amurka

mahakauciyar Guguwar a Amurka da ta janyo katsewar wutar Lantarki a wasu sassan yankunan kasar
mahakauciyar Guguwar a Amurka da ta janyo katsewar wutar Lantarki a wasu sassan yankunan kasar

An samu mutuwar mutane akalla 45 tare da katsewar wutar Lantarki ga Miliyoyin mutane sanadiyar mahaukaciyar guguwar da ta shafi kasar Amurka. Guguwa mafi muni da aka samu a kasar da ta janyo hasarar Biliyoyin daloli.

Talla

Miliyoyin mutane ne ke zama cikin duhu wasu kuma da dama ke cikin ambaliyar ruwa a yankin birnin New York da gabacin Amurka.

Adadin wadanda suka mutu sun kai mutane 45 a Amurka da Canada, kwanaki bayan mutuwar mutane 69 a yankin Caribbean kafin guguwar ta cim ma gabacin Amurka.

Guguwar ta shafi yankin New Jersey da yankin New York da Manhattan. Al’amarin da ya sa aka dakatar da da duk wasu ayukka a yankunan.

Wata hukuma mai yin kididdigar hasarar da aka tafka a lokutan hadururruka dake kasar Amurka, ta yi hasashen an tafka hasarar kudi Dalar Amurka Biliyan 20 sanadiyar guguwar.

A cewar shugaban hukumar ta Eqecat, Bill Keogh, sun samu wannan kididdiga ne daga bayanan farko da suka tattara inda ya kara da cewa, sai nan gaba za a fitar da sauran bayanai da suka shafi hasarar kayayyaki, da rufe wuraren kasuwanci.

A yanzu haka masana tattalin arziki na kara ikrarin cewa hasara da za tafka daga karshe za ta iya kai wa yawan kudi Dalar Amurka 30 zuwa 50.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI