Isa ga babban shafi
Algeria-Faransa

Algeria ta nemi Faransa ta amsa laifukan da ta aikata

Wasu Al'ummar Algeria a lokacin da suke gudanar da Zangar Zangar la'antar laifukan da Faransa ta aikata a lokacin yain samun 'Yancin kasar bayan cika shekaru 50
Wasu Al'ummar Algeria a lokacin da suke gudanar da Zangar Zangar la'antar laifukan da Faransa ta aikata a lokacin yain samun 'Yancin kasar bayan cika shekaru 50 Reuters/Louafi Larbi
Zubin rubutu: Bashir Ibrahim Idris | Awwal Ahmad Janyau
1 min

A yau Alhamis kasar Algeria ke bukin tuna yakin da kasar ta gwabza shekaru 58 da suka gabata, domin samun ‘Yancin kai daga hannun Faransa, matakin da ya yi sanadiyar kashe daruruwan mutane. Ministan da ke kula da mazan jiyan Algeria, Mohammed Cherif Abbas, ya bukaci Faransa ta amince a hukumance kan kisan da aka yi wa ‘Yan kasar a wancan lokaci.

Talla

Tuni dai shugaban Faransa, Francois Hollande, ya amince da cewa ‘Yan Sanda sun yi amfani da karfin da ya wuce kima kan masu zanga zangar neman ‘Yancin Algeria a watan Oktoban shekarar 1961.

Masana Tarihi sun ce tsakanin mutane 50 zuwa 200 ne aka kashe a lokacin yakin neman ‘Yancin kasar Algeria.

A watan Disemba ne aka sa ran shugaban kasar Faransa Francois Hollande zai kai ziyara kasar Algeria domin inganta dangata tsakanin kasashen Biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.