Faransa-Syria-EU

Faransa ta Bukaci EU nazarin haramtawa ‘Yan tawayen Syria makamai

Mayakan da ke yaki da Gwamnatin Bashar al Assad na Syria
Mayakan da ke yaki da Gwamnatin Bashar al Assad na Syria REUTERS/Zain Karam

Kasar Faransa tace za ta bukaci kungiyar kasashen Turai ta yi nazarin dokar hana bai wa ‘Yan Tawayen Syria makamai, don taimakawa wadanda ke yaki da gwamnatin shugaba Bashar al Assad.

Talla

Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius ne ya sanar da matsayin na gwamnatin kasar, inda ya ke cewa saboda dokar hana bai wa kasar makamai, babu yadda za su taimakawa ‘Yan Tawayen daga kasashen Turai.

Fabius yace, saboda bukatar samun makaman da ‘Yan Tawayen suka bukata, ya zama wajibi a janye dokar, kuma za su gabatar da ta su bukatar ga sauran kasashen Turai, domin amince wa da ita.

Rikicin kasar Syria

Ministan yace, basa fatar ganin yaduwar makamai a kasar, amma kuma tunda akwai Yankunan da ‘Yan tawayen suka kama, kuma gwamnati na ci gaba da kai musu hari a wuraren, ya zama wajibi a ba su makamai su kare kansu.

Ana sa ran shugaba Francois Hollande zai gana da shugabanin Yan Tawayen, a karkashin Ahmed Moaz al-Khatib ranar asabar mai zuwa, a birnin Paris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.