Isa ga babban shafi
Faransa-Falestine-MDD

Faransa tace za ta goyi bayan kudirin Falesdinawa a MDD

Tutar Isra'ila da Tutar Falesdinawa
Tutar Isra'ila da Tutar Falesdinawa
Zubin rubutu: Bashir Ibrahim Idris | Awwal Ahmad Janyau
2 min

Kasar Faransa ta bayyana shirinta na goyan bayan bukatar Falesdinawa na samun kujerar Yan kallo a zauren Majalisar Dinkin Duniya. Falesdinawa sun yaba da matakin a kokarin da suke yin a neman samun goyon bayan kasashen Duniya.

Talla

Duk da Faransa Aminiyar Amurka ce da ke adawa da kudirin, amma Ministan harakokin wajen kasar Laurent Fabius yace Faransa za ta bada goyon bayanta domin ganin samun ‘Yancin Falasdinawa.

Kasar Faransa tana cikin kasashe Biyar masu kujerar Din Din a Majalisar Dinkin Duniya, Kuma Mista Fubius yace Faransa za ta kada kuri’ar Amincewa da kudirin Falestine.

Yanzu haka dai kasar Faransa ita ce kasa ta farko daga kasashen Turai da ta fito ta ayyana goyon bayan samun ‘Yancin Falesdinawa a Zauren Majalisar Dinkin Duniya. Amma kuma sai kudirin na Falesdinawa ya samu amincewar kasashen Mambobin Majalisar 193.

Idan dai har Falesdinawa suka cim ma wannan kudirin zai basu damar zama mambar Kotun hukunta manyan laifukan yaki ta Majalisar Dinkin Duniya domin kalubalantar Isra’ila da ta mamaye yankunansu a gabar yamma da kogin Jordan.

A zamanin Mulkin Sarkozy a Faransa Falesdinawa sun samu wakilci a hukumar UNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya a bara, kuma Mista Fubius yace amincewa da Falesdinwa yana cikin muradun Shugaba Francois Hollande.

Amurka da Isra’ila da kawayensu suna cikin manyan kasashen da ke adawa da kudirin wadanda kuma za su yi kokarin dakile duk wata hanya da Falesdinawa za su bi don cim ma gurinsu.

Amma kuma masana Diflomasiya sun yi hasashen kasashen Turai 11 cikin 15 za su kada kuri’ar amincewa da kudirin na Falesdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.