Philippine

Mahaukaciyar Guguwa ta kashe daruruwan mutane a Philippines

Gawawwakin mutanen da suka mutu sakamakon baka'in guguwar Bopha da ta shafi Philippines
Gawawwakin mutanen da suka mutu sakamakon baka'in guguwar Bopha da ta shafi Philippines REUTERS/Karlos Manlupig

Akalla mutane kusan 500 aka ruwaito sun mutu wasu da dama kuma suka salwanta sakamakon bala’in guguwa da ruwan saman da a ka samu a kasar Philippines kamar yadda hukumomin kasar suka sanar.

Talla

A yankunan New Bataan an ruwaiton samun mutuwar mutane 258 wasu kuma kimanin 241 suka salwanta sanadiyar Guguwar da ake kira da sunan Bopha.

Haka kuma a yankin Davao an ruwaito mutuwar mutane 81.

Masana sun ce Wannan guguwar ita ce mafi karfi da ta afkawa kasar Philippines a bana kuma tana tafiya ne dauke da iska mai gudun kilomita 210 a duk sa’a daya.

Akalla mutane 43 suka mutu bayan zaizayar kasar da ta biyo bayan hakan, a kusa da wani sansanin sojin kasar, wasu mutane sama 20 suka samu raunuka.

Guguwar wacce tafi aukuwa a gabacin kasar ta, a cewar rahotanni, ta zo da ruwa da dama a yayin da ta yi ta tunbike bishiyoyi da rufin gidaje tare da katse wutan lantarki, wanda hakan ya yi sanadiyar ficewar mutane sama da 56,000 daga mahallinsu a yankin.

Bayanai sun nuna cewa, akalla jiragen sama kusan 150 guguwar ta hana tashi a yankin Mindanao, a yayin da fiye da mutane sama da 3,000 wadanda ke kokarin tafiya a jiragen ruwa ke jibge a tashar jiragen ruwa daban daban a yankin.

Wani mazaunin garin da ake kira Tagum, ya fadawa kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa wannan shi ne karo na farko da suka taba fuskantar irin wannan bala’i.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.