Koriya ta Arewa

Koriya ta Arewa ta yi nasarar harba tauraronta a samaniya

Tauraron da Koriya ta harba a samaniya
Tauraron da Koriya ta harba a samaniya

Kasar Korea ta Arewa ta yi nasarar Harba tauraronta na Roka duk da gargadin takunkumi da kasashen Duniya suka yi wa kasar. Kasashen China da Rasha sun bayyana takaicinsu bayan Korea ta Harba Rokan kamar yadda kasar Amurka ta yi Allah Waddai da matakin a matsayin barazana ga tsaro.

Talla

Jekadun Kasashen Yammacin Duniya sun ce, Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniyar zai gudanar da wani taron gaggawa, don nazarin yadda Korea ta Arewa ta harba roka zuwa sararin samaniya, duk da takunkumin da aka kakabawa kasar.

Daya daga cikin Jakadun, yace kasashen Japan da Amurka ne suka bukaci gudanar da taron da misalin karfe 11 na safe agogon Amurka, karfe 5 agogon GMT a yau Laraba.

Darajar Kudin Yen ta fadi jim kadan bayan Koriya ta bayyana samun nasarar harba Tauraron.

Shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-Un yaa harba Tauraron ne domin bukin cika shekara da mutuwar mahaifin shi tsohon shugaban kasa Kim Jong-Il wanda ya mutu a ranar 17 ga watan Disemba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.