Amurka

Wani dan Bindiga ya kashe wasu mutane biyu a Amurka

Gobarar da ta tashi inda kuma William Spengler, ya bindige masu aikin ceto a Webster
Gobarar da ta tashi inda kuma William Spengler, ya bindige masu aikin ceto a Webster REUTERS/Jamie Germano

Wani Dan bindiga ya kashe jami’an kwana-kwana guda biyu, tare da raunata wasu mutane biyu, bayan ya bude masu wuta a lokacin da suka kawo gudunmawa, yayin wata gobarar da ta tashi a birnin New York din kasar Amurka.

Talla

Harin na ranar jajibirin kirsimeti, na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan yadda za a takaita Mallakar bindigogi a kasar, bayan da wani matashi ya hallaka mutane 26 a wata makaranta a birnin Newtown da ke jihar Connecticut.

Binciken da jami’an tsaro suka gudanar ya gano cewa, mutun daya ne ya kai harin, kuma daga bisani an ga gawar shi da raunukan da ya samu bayan ya bude huta

Babban Jami’in ‘Yan sanda a yankin Webster Cif Gerald Pickering yace dan bindgar sunan shi William Spengler mai shekaru 62 na haihuwa. Kuma ‘Yan sandan sun ce an taba yanke masa hukuncin daurin shekaru 17 bayan bindige Kakar shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.