Brazil

‘Yan fashi sun yi garkuwa da mutane 9 Brazil

'Yan sandan kasar Brazil a lokacin da suke tisa keyar wani mai laifi
'Yan sandan kasar Brazil a lokacin da suke tisa keyar wani mai laifi Ảnh: REUTERS/Sergio Moraes

‘Yan sandan kasar Brazil sun ce, ‘Yan fashi da makamin sun afka wa wani wurin aikin lu’ulu’u, inda suka tafi da mutane 9, suka yi garkuwa da su.

Talla

Wani jami’in soja ya shaida wa kamfanin dillacin labarum Faransa na AFP cewa 3, daga cikin mahara sun mutu yayoin bata kashin da aka yi a jihar Rio Grande do Sul.
 

Jami’in sojan yace maharan sun dauke mutanen zuwa cikin dazuka, inda ‘yan sanda cikin motoci da jiragen sama masu saukar ungulu suke ci gaba da neman su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.