Algeria-Mali

Mutane 34 sun mutu cikin wadanda aka yi garkuwa da su a Algeria

Kamfanin Gas na Amenas, inda aka yi garkuwa da 'Yan kasashen wajen kamin dakarun Algeria su kai harinsu
Kamfanin Gas na Amenas, inda aka yi garkuwa da 'Yan kasashen wajen kamin dakarun Algeria su kai harinsu Reuters

Akalla mutane 34 cikin ‘yan kasashen wajen da masu kishin Islama ke garkuwa da su kasar Mali tare da wasu masu kishin Islama su 15 sun hallaka bayan wani hari da dakarun kasar Alegria suka kai wani sansanin ‘yan tawayen. Rahotanni har sun nuna cewa, mutane 7 daga cikin ‘yan kasashen waje da ake garkuwa da su sun sami kubuta.  

Talla

Bayanan na cewa wadan da aka sami kubutar dasu sun hada da ‘Yan Britaniya 2, da dan Faransa, da dan kasar Kenya.

Hukumomi a kasashen Birtaniya, Faransa da Norway, tun farko sun tabbatar da cewa ana kan kai harin a lokacin.

A wayewar garin Alhamis ne, sojojin kasar ta Algeria, suka bayyan cewa sun yi wa wasu ‘Yan bindiga Kawanya da suka yi garkuwa da mutane sama da 150 hadi da wasu ma’aikatan Kamfanin Mai ‘Yan kasashen waje sama da 40, bayan sun hallaka uku daga cikinsu.

A cewar Kamfanin Dillacin Labaran kasar Mauritania na Sahara Media da ANI, Mayakan na kasar Alegria, sun kai hari ne domin mayar da martani ga gwamnatin kasar, saboda ba kasar Faransa damar amfani da sararin samaniyarta wajen kai wa ‘Yan tawayen Mali hari.

Mayakan dai sun bukaci da a kawo karshen yaki a Mali kafin su mika mutanen da suka yi garkuwan da su.

Rahotanni sun ce Mayakan sun kai harin ne a Kamfanin Man Algeria na In Amenas wanda ke aikin hadin gwiwa da Kamfanin BP na Birtaniya da Kamfanin Statoil na Norway.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.