Venezuela-Bolivia

Shugaban Bolivia yace Chavez yana samun sauki

Shugaban kasar Bolivia Evo Morales, yace ana matakin karshe na jinyar cutar Cancer ko Sankara, da ake wa shugaban Venezuela Hugo Chavez, a kasar Cuba, kuma yana gab da komawa gida.

Dubban Masoyan Hugo Chavez à birnin Caracas
Dubban Masoyan Hugo Chavez à birnin Caracas REUTERS/Carlos Garcia Rawlins
Talla

Mista Morales, ya fadi haka ne a lokacin da ya ke gabatar wa majalisar dokokin kasar Bolivia rahoto, kan cikar shi shekaru Takwas a karagar mulkin, inda yace ya yi Magana da hukumomin kasar Cuba game da jinyar Chavez, ba tare da yin Karin bayani ba.

Chavez mai shekaru 58, ya yi sanadiyyar hade kan gwamnatocin yankin Latin Amurka, masu ra’ayin gurguzu, da ke kokarin dakile ingizon da Amurka ke da shi a yankin kuma Morales aminin shi ne, na kut-da-kut.

Sai dai Ministan yada labaran Venezuela Ernesto Villegas yace duk da labaru masu bayar da kwarin gwiwa kan lafiyar shugaban, har yanzu ba a sa ranar dawowar shi gida ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI