Brazil

Ana zaman makoki a kasar Brazil bayan mutuwar mutane sama da 200 a gobara

Masu aikin 'yan kwana-kwana suna kashe gobarar da ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 200 a kasar Brazil
Masu aikin 'yan kwana-kwana suna kashe gobarar da ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 200 a kasar Brazil

A yau litinin ‘yan kasar Brazil na zaman makokin mutane 230, da suka rasa ransu a wata gobarar da ta tashi a wani gidan rawa, lamarin kuma da ya yi sanadiyyar raunata wasu fiye da 100.

Talla

Wadanda suka tsira da ransu, da yawansu daliba ne a fannin kimiyya, sun bayyana yadda aka yi ta take abokan karatunsu, a yayin gobarar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsu.
 

Ministan lafiyan kasar Alexandre Padilha, ya ce ana kokarin ceto ran wadanda suka sami raunuka, da rahotanni ke cewa da dama na cikin halin mutu ko-koi-rai-ko-koi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.