Iran

Iran ta nemi tattaunawa da kasashen duniya akan makamin nukiliyanta

Shugaban kasar Iran, Mahmoud Ahmedinejad.
Shugaban kasar Iran, Mahmoud Ahmedinejad. (Photo : AFP)

Kasar Iran ta bayyana gudanar da sabuwar bukatar tattaunawa da kasashen Duniya kan shirin ta na makamashin Nukiliya, tare da bayyanawa karara cewar ta amince da bukatar da kasar Amurka ta fitar na gudanar da tattaunawar kai tsaye da juna idan hakan zai yi amfani. Ministan harkokin wajen kasar Iran, Ali Akbar Salehi, ya ce kasashen masu karfin tattalin arziki na Duniya guda shida sun shirya a koma teburin shawara ne a kasar Kazakhstan ran 25 ga watan Fabrairu. 

Talla

Ko a shekarar da ta gabata ma kasar ta Iran ta gudanar da tattaunawa kashi uku da wadannan manyan kasashen Duniya da suka hada da Amurka da China da Rasha da Birtaniya da Faransa da kuma Jamus.

Tattaunawar dai ta mai da hankali ne ga batun takaddamar da ake da ita kasar Iran kan batun makamashin Nukiliya da Iran ta tsaya akan cewar bana tada hankali bane.

Sai dai har yanzu ba’a samu tantancewa da sabon wa’adin da aka shata ba daga Ofishin hukumar kula da Kungiyar Tarayyar Turai domin gudanar da wannan taron ba.

Ali Akbar Salehi ya ce a nasu bangaren ba gudu-ba-ja da baya ga batun tattaunawa, musamman idan akwai kyakkyawar manufa game da taron.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.