korea ta Arewa

Korea ta Arewa ta yi nasarar gwajin Makamin Nukiliyarta

Tauraron Korea ta Arewa (KSLV-I satellite)
Tauraron Korea ta Arewa (KSLV-I satellite) AFP

Gwamnatin kasar Korea ta Arewa ta tabbatar da samun nasarar gwajin makamin Nukiliyarta, al’amarin da kasashen Duniya suka yi Allah Waddai da shi. Akwai taron gaggawa da Kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya ya kira domin tattauna daukar matakai akan Korea ta Arewa.

Talla

Kamfanin Dillacin labaran kasar ya ce an samu nasarar gwajin makamin Nukiliya karo na uku.

Gwamnatin Korea ta Arewa tace ta yi gwajin ne domin inganta tsaro da ‘Yancin kasar daga Amurka da ke adawa da ‘Yancinsu na harba tauraro a sararin samaniya.

Ana sa ran Kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya zai yi Allah waddai da gwajin Makamin tare da karfafa takunumi ga kasar Korea ta Arewa.

A baya Korea ta Arewa ta gudanar da gwajin Nikiliyarta a shekarar 2006 da 2009, matakin da kasar Amurka da Korea Ta Kudu da kasashen Turai suka la’anta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.