MDD-Korea Ta Arewa

Kwamitin Sulhu ya yi Allah Waddai da gwajin Nukiliyar Korea ta Arewa

Wani yana kallon yadda Korea ta Arewa ta harba Makaminta a Telebijin
Wani yana kallon yadda Korea ta Arewa ta harba Makaminta a Telebijin REUTERS/Kim Hong-Ji

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi alkawarin daukar matakin da ya dace akan kasar Koriya ta Arewa, saboda gwajin makamin nukiliyar da kasar ta yi jiya bayan wani taron gaggawa da kwamitin ya gudanar jiya, kwamitin yace ya fara aiki kan irin matakan da suka dace ya dauka akan kasar.