Birtaniya

Wani shugaban darikar katulika ya yi murabus

Paparoma Benedict
Paparoma Benedict REUTERS/Wolfgang Rattay

A yau din nan ne wani Shugaban darikar Catolika mafi girma a Britania, Cardinal Keith O’Brien yayi murabus , sakamakon zarge-zarge da ake masa na rashin halayen kwarai.Shidai Cardinal Keith O’Brien shine Archbishop na St. Andrews da Edingburgh, kuma shugaban churchin Scotland, tun a shekara ta 1980 ake zargin sa da zina.Ya kasance shine daya rak daga yankinsa, da zai jefa kuriar zaben sabon Paparoma.