Iraqi-Amurka

Mutane 120,000 aka kashe a Iraqi tare da yin hasarar kudi dala Biliyan 800-Bincike

Mutum Mutumin Tsohon Shugaban Iraqi Saddam Hussein wanda aka karya bayan an rataye shugaban
Mutum Mutumin Tsohon Shugaban Iraqi Saddam Hussein wanda aka karya bayan an rataye shugaban © Reuters

Wasu alkalumman masana da aka wallafa a kwanakin nan, sun ce akalla fararen hula 116,000 da dakaru 4,800 suka mutu a yakin Iraqi a tsakanin 2003 har zuwa ficewar Dakarun Amurka a 2011. Sakamakon binciken yace kasar Amurka ta yi hasarar Kudi Dala Biliyan 810.

Talla

Wasu Farfesa ne guda biyu a kasar Amurka suka gudanar da bincike wadanda suke  ke yi sharhi a mujallar Birtaniya ta The Lancet.

Masanan sun ce sun tattara alkalumman ne daga rahotannin kafafen yada labarai da kungiyoyi masu zaman kansu da ke aiko da rahoto game da yakin Iraqi.

Binciken masanan yace dubban mutane ne suka jikkata sannan fiye da mutane Miliyan biyar aka raba da gidajensu a yakin Iraqi.

Masanan sun dangata alkalumman bincikensu da shafin intanet na costofwar.com.

A cewar Farfesa Barry Levy na Jami’ar likitanci ta Boston da kuma Farfesa Victor Sidel na Kwalejin Albert Einstein a New York, kudaden da Amurka ta kashe a yakin Iraqi sun isa a inganta fannin lafiya a kasar.

A wasu alkalumma da hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar game da rikicin Iraqi a 2008, an bayyana cewa adadin mutanen Iraqi 104,000 zuwa 223,000 suka mutu tsakanin watan Maris na 2003 zuwa watan Juni na 2006.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI