Afghanistan

Shugaban Afghanistan ya gana da Sarkin Qatar

Shugaban Afghanistan, Hamid Karzaï.
Shugaban Afghanistan, Hamid Karzaï. REUTERS/Susan Walsh

An gudanar da tattaunawa a yau lahadi tsakanin shugaban kasar AfghanIstan Hamid Karzai da kuma sarkin kasar Qatar Sheik Hamid bin Khalifa Al-thani a birnin Doha domin share fagen bai wa kungiyar Taliban damar bude ofishinta a kasar ta Qatar.

Talla

A can baya dai shugaban kasar ta Afghanistan sau da dama yana bayyana rashin amincewarsa da bai wa kungiyar ta Taliban wadda kasashen duniya cikinsu kuwa har da Amurka babbar abokiyar kawancen Qatar ke kallo a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda damar buda ofishi a kasar ta Qatar.
To sai daya daga cikin dalilan da suka sa kasar ta Qatar ta amince da bai wa Taliban wannan dama kamar dai yadda bayanai ke nuni, shi ne yadda shugabannin kungiyar suka ce ba za su taba yin tattaunawar kai-tsaye da gwamnatin Karzai ba.
Batun buda ofishin na Taliban a wannan kasa da ke yankin tekun Fasha, ya zo ne a daidai lokacin da kasashen kungiyar tsaro ta Nato da ke mamaye da Afghanistan ke shirin janye dakarunsu daga kasar a cikin shekara mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.