Duniya

Hukumar Lafiya ta Duniya na kokarin kakkabe Shan-inna a duniya

Alamar Hukumar Lafiya ta Duniya
Alamar Hukumar Lafiya ta Duniya

Hukumar lafiyar ta WHO ta ce tana fatar cimma kudirin magance cutar shan-inna ko kuma Polio kafin shekarar 2018.

Talla

Sannan hukumar ta ce barazanar tsaro da jami’an lafiya ke fuskanta game da rigakafin cutar a Najeriya da Pakistan shi ne babbar damuwarta.
Hukumar ta ce cutar Shan-inna ta fi kamari ne a kasashen Afghanistan, Najeriya da kuma Paksitan inda hukumar ta yi fatar kawo karshen matsalar kafin karshen 2014.
Hukumar ta ce an samu raguwar cutar a bara idan har aka kwatanta da shekarar 2011
Hukumar WHO dai ta kaddamar yakin da cutar Shan-inna ne a shekarar 1988 bayan ta shafi kasashe sama da 125 kuma cutar ta shafi yara kanana kimanin 350,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI