Libya-MDD

Rikicin Libya ya taimaka wajen kwararar makamai a rikicin Syria da Mali-MDD

Wasu 'Yan tawayen kasar Libya
Wasu 'Yan tawayen kasar Libya

Wani Rahotan Majalisar Dinkin Duniya, yace makaman da ke fitowa daga kasar Libya, su ke haifar da tashin hankali a kasashen Syria da Mali, saboda yadda suke fadawa hannun Yan ta’adda.

Talla

Wani rahoton masana a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya wadanda suka sa ido a takunkumin da aka kakabuwa Libya a lokacin zanga-zangar kin jinin gwamnatin Marigayi Kanal Gaddafi sun ce rikicin kasar ya taimaka wajen kawarar makamai a yankin.

Rahotan da masanan suka rubutawa kwamitin Sulhu, yace Libya ta zama hanyar samun makamai a Yankin, saboda guguwar Gwamnatin kasar, da kuma yadda kungiyoyin da ke dauke da makamai ke cigaba da adawa da Gwamnati.

Rahotan yace, akasarin tashe tashen hankalun da ake samu a Afrika, na da nasaba da makaman da ke fitowa daga Libya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI