Amurka-Marathon

Bama bamai sun kashe Mutane uku tare da raunata sama da 100 a harin Boston

Harin Marathon a Boston kasar Amurka
Harin Marathon a Boston kasar Amurka REUTERS EXCLUSIVE REUTERS/Dan Lampariello

Akalla mutane uku aka ruwaito sun mutu kuma wasu mutane sama da 100 suka jikkata sakamakon fashewar bama bamai guda biyu a gasar tseren gudun Marathon da ake gudanarwa a Boston a kasar Amurka. Har yanzu ana gudanar da bincike domin gano wadanda suka dasa bama baman.

Talla

Har yanzu ana lalaben wadanda suka dasa bama baman da suka tashi guda biyu. Kodayake an ji karar na uku amma jami’an tsaro sun ce yana da nasaba da wuta.
Jami’an tsaron Amurka sun ce sun yi nasarar warware wasu bama baman guda biyu da aka dasa.

Lamarin ya faru ne a lokacin da ‘Yan tseren gudun na Marathon suna zangon karshe.
Wannan ne karo na 117 da ake gudanar da gasar tseren gudun na Marathon a Boston, wanda shi ne wasa na biyu da ke jan hankalin Amurkawa bayan wasan Super Bowl.

‘Yan tseren gudu kimanin 28,000 ne suka shiga gasar daga yankunan Amurka da kuma wakilai daga kasashe sama da 90.

‘Yan tseren gudun Kenya ne a kan gaba.

Kuma ana gudanar da tseren gudun ne a dai dai lokacin da gwamnatin Jahar Massachusetts ta ware hutu domin tunawa da karrama juyin juya halin Amurka a wajajen 1775.

Wannan dai shi ne hari mafi muni da aka kai tun bayan harin 11 ga watan Satumba. Shugaban Amurka Barack Obama yace za su yi farautar wadanda suka kai hare haren a cikin ‘yan kallo da suka tsaya saman tituna suna kallon tseren gudun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI