Amurka

'Yan sandan Amurka sun kashe cikin wadanda ake zargin sun kai harin Boston

Dan Sandan Amurka ya taka bindiga a watertown Massachusetts bayan kisan dan sanda a cbiyar fasaha ta da ke Cambridge.
Dan Sandan Amurka ya taka bindiga a watertown Massachusetts bayan kisan dan sanda a cbiyar fasaha ta da ke Cambridge. REUTERS/Brian Snyder

'Yan sandan Boston sun tabbatar da kisan cikin wadanda ake zargin sun kai harin Marathon. Yanzu haka 'Yan sandan Boston na ci gaba da farautar daya daga cikin wadanda ake zargi  bayan sun kai samame a yankunan Massachusetts.  

Talla

Wannan na zuwa ne bayan Hukumar Bincike ta FBI ta nuna hoton wasu mutane biyu da ake zargin sun kitsa kai harin wanda ya kashe mutane uku tare da raunata sama da 170.

Akwai ruwan albarussai da ake yi a Boston bayan kisan wani Dan sanda a Cambridge,
 inda aka nuna hoton gawar wani matashi malale a kasa ‘Yan sanda sun kewaye shi.

Amma ‘Yan sandan Massachusetts sun ce zasu bi gida gida suna bincike domin farautar wadanda suka kai harin.

A lokacin da ake gabatar da hotunan mutanen, hukumar bincike ta FBI ta nemi taimakon ‘Yan kasa domin tantance mutanen da aka nuna rike da jika da hular wasan Baseball cikin mutane kafin Bama baman su tashi.

Nuna hotunan na zuwa bayan shugaban Amurka Barack Obama ya gabatar da jawabin juyayin wadanda suka mutu a Boston.

Cikin mako guda dai Amurka ta gamu da bubuwa da dama, inda kwanaki biyu bayan kai harin Boston, aka cafke wani mutum da ake zargin ya aika da wasika mai dauke da guba zuwa ga Obama. Akwai kuma gobara da aka samu a biyar sarrafa takin Zamani a Texas da ta yi sanadiyar mutuwar mutane 14.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI