Amurka-Marathon

Har yanzu ba a gano dalilin kai harin Marathon ba a Boston

'Yan uwan juna da ake tuhumar sun kai harin Boston a lokacin da ake gudanar da tseren gudun Marathon
'Yan uwan juna da ake tuhumar sun kai harin Boston a lokacin da ake gudanar da tseren gudun Marathon Reuters

Masu Gabatar da kara a Amurka, basu bayyana dalilin da ya sa Dzokhar Tsarnaev da dan uwansa suka kai harin bom Boston ba, a wasu takardun shaidar kara da suka gabatar. Amma an tuhumi Tsarnaev da anfani da makamin kare dangi da kuma lalata dukiyar jama’a abinda ya kai ga rasa rayuka.

Talla

Ana iya yanke wa Dzokhar Tsarnaev hukucin kisa kan kowanne daga cikin wadannan tuhumomin.

Duk cewa yana kwance a gadon Asibiti amma Dzokhar Tsarnaev mai shekaru 19 ya amsa tambayoyi ta yin amfani da girgiza kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI