Amurka-Iraqi

Sojan Amurka ya amsa kashe Sojojin Iraqi 5

Wani Sojar Iraqi a kusa da inda aka kai hari a Bagadaza
Wani Sojar Iraqi a kusa da inda aka kai hari a Bagadaza

Wani Sojan Amurka Saje John Russell, ya amsa kashe sojojin kasar Iraqi biyar, a wata shari’ar soji da zai sa a kaucewa aiwatar ma sa da kisan kai. Ana tuhumar Saje Russell ne da harbe wasu sojojin Iraqi da ke aiki a cibiyar kula da lafiya, a shekarar 2009.

Talla

Lauyoyinsa sun shiga kulla yarjejeniya da ma su gabatar da kara, kan cewar muddin ya amince da tuhumar da ake masa, to ba za’a aiwatar masa da hukuncin kisa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI