Madagascar

An fara taron sassanta yan siyasa a Madagascar

Andry Rajoelina, Shugaban kasar Madagascar
Andry Rajoelina, Shugaban kasar Madagascar rfi

A Madagascar ana gab da cima matsaya ta sassanta yan siyasa, kungiyoyin fararen hula da sojin kasar wata dama dake iya kawo karshen cece kuce siyasa a kasar.Comity sassanta yan kasar Madagascar CRM ne ya dau alhakin gudanar da taron a  yau  bayan da aka wace baram-baram a shekara ta 2009 lamarin da haifar da juyin mulkin a lokacin . Shugaban kasar kuma dan takara a zaben shugabanci Andre Rajolina da bai samu halartar zauren taron ba ya bayana gamsuwar sa, ta bakin kakakin sa ya bukacin mahalarta taron da sun yi watsi da batun na cewa ya sauka daga mukami shugabanci kasar kafi zaben na  ranar asiri da hudu na watan yuli na wanan shekara.Hukumar Majalisa Dukin Duniya ta dakatar da taimakon ta na kudade dangane da zaben kasar Madagascar har sai yan siyasar kasar sun cima matsaya.