Syria-MDD

Fabius ya ce tabbas an yi amfani da makamai masu guba a Syria

Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius
Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius REUTERS/Charles Platiau

Duk da cewa Laurent Fabius, bai bayyana wuri ko kuma akan su waye aka yi amfani da makaman da ke kunshe da samfurin sarin mai guba ba, to amma dai ya ce lamarin ya faru ne a wurare daban daban a cikin kasar ta Syria.

Talla

Ministan na harkokin wajen Faransa, ya ce wani dakin bincike da ke kasar ya gudanar da gwaje-gwaje wadanda sakamakonsu ya yi nuni da cewa akalla an yi amfani da wannan sinadiri a wata unguwa da ke wajen birnin Damascus da kuma wani gari mai suna Saraqeb a arewa maso yammacin Syria.

Bisa ga dukkan alamu dai kalaman na minista Fabius, suna ishara ne da samfurin da ake zaton cewa akwai guba a cikinsa wanda wasu ‘yan jaridar Le Monde da suka gudanar da aiki a Syria suka dawo da shi a Faransa a cikin wata Afrilun da ya gabata, inda daga bisani aka tabbatar da cewa ko shakka babu guba ce da ke cikin makaman da aka yi amfani da su ne a yakin na Syria.

Ministan na Faransa ya ce tuni ya mika wa hukumomin Amurka da sakamakon wannan bincike domin kara tabbatar da ko samfurin na Sarin ne ko kuma a’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI