Isra'ila-Felesdinu

Isra’ila ta bayyana cewar Mahmood Abbas na kulla dangantakar kasa-da-kasa

Shugaban Palesdinwa Mahmud Abbas tareda babban Jigon kasar China
Shugaban Palesdinwa Mahmud Abbas tareda babban Jigon kasar China REUTERS/Jason Lee

Gwamnatin kasar Isra’ila ta yi zargin cewar Shugaban Falesdinawa Mahmoud Abbas na kokarin cimma bukatun samun cin gashin kai ba tare da bin hanyar sulhu ba. Kamar yadda mataimakin Ministan harakokin wajen Isra’ila ya fito yana fada a kafar yada labarai Plasdinu na shirin kulla hudayyar kasa-da-kasa abinda zai kawo tangarda ga manufofin Israela da Amurka akan kasar ta Palasdinu.

Talla

Wannan zargin dai na Isra’ila na zuwa ne, kwanaki kalilan bayan da sakataren harakokin wajen kasar Amurka John Kerry ya kai ziyara karo na Biyar domin tattauna fito da hanyoyin zaunawa teburin sasantawa tsakanin Isra’ila da Falesdinawa.
A Watan Nuwamba ne Palesdinu ta gabatar da bukatar samun matsayi a babban Zauren Majalisar dunkin Duniya daga zamanta na ‘yar kallo zuwa matsayin mamba a Zauren.

Wannan matsayin dai ya sha suka daga bangaren Hukumomin Israela dana kasar Amurka masu kallon Israela a matsayin Saniyar ware.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI