Amurka

Susan Rice zata kasance sabuwar mai bada shawara kan sha’anin tsaro ta kasar Amurka

Susan Rice ke jawabi a ran 12 ga Fabrairun 2013.
Susan Rice ke jawabi a ran 12 ga Fabrairun 2013. REUTERS/Eduardo Munoz

Shugaba Barack Obama zai bayyana sunan Susan Rice a matsayin sabuwar mai bada shawara kan sha’anin tsaro ta kasar Amurka ‘yan Watanni kalilan bayan da ake ganin cewar al’amurran Benghazi na shirin kawar da fatar da ake ta kasancewarta a matsayin Jakadar kasar Amurka a kasashen waje.

Talla

A watan Yuli ne dai Rice zata maye gurbin Tom Donilon wanda ke zaman mai daiwa Obama shawara a wannan lokaci, a wani bangare na sake fasalin tsarin manufofinsa na kasashen waje.

Wannan al’amarin dai ya kasancewa Rice tamkar wani yanayi na komal-baya bayanda aka dan maida ita gefe a shirin maida ita Sakatariyar harkokin wajen Barak Obam a farkon wannan Shekarar.

Wani babban jami’in kasar Amurka ya bayyana cewar bada jimawa ba ne Shugaban kasar Amurkan zai bayyana cewar bayan shekara hudu, yanzu Tom Donilon zai bar aikin bada Shawara a hukumar tsaro ta kasar Amurkan a Watan Yuli, kuma Ambassada Susan Rice ce zata maye gurbin sa.

Hakama jami’in ya bayyana cewar shugaba Barack Obama zai bayyana sunan Samatha Power data kasance tsohuwar kwararriya kan harkokin da suka shafi manufofin kasashen waje ta kasar Amurka a matsayin wadda zata mayegurbin Samatha

Donilo ya kasance bangaren shugaba Barack Obama tun bayan day a shiga Fadar White House a shekarar 2009, sanda yam aye gurbin James Jones a shekar 2010, kuma ya kasance dai daga cikin gwanayen da suka yi tsaye ga kulla dangantakar kasar Amurka da China, kuma a baya-bayan nan ma yayi tafiyayyiya zuwa kasar China domin shirya tafiyar shugaba Xi Jinping zuwa Jihar Califonia.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI