Tarayyar Turai-Siriya

EU ta dauki nauyin kara kudaden talafin zuwa Syria

rfi

Kungiyar Tarayyar Turai ta bada sanarwar kara kudaden tallafi kimanin Miliyan 400 ga Syria da kuma kasashen da ke makwabtaka da ita wadanda ke fama da kwararar ‘Yan gudun hijira. Shugaban hukumar Jose Manuel Barroso yace rikicin Syria rikici ne da har yanzu ba’a san ranar kawo karshen shi ba.Lamarin kasar  Syria  na  ciggaba  da  tayar  da  hankulan  kasashen  nahiyar  Turey,duk  da kiran da  Shugaban  faransa  Francois  Hollande  yayi  zuwa  kasashen Duniya  na  daukar  mataki  ga  gwamnatin  kasar  Syria  gani  hujjojin da  Faransa  keda  su na  cewar  Gwamnatin Syria  ta  yi  amfani da  guba  ga  yan kasar ta.