EU-China

Jamus ta bukaci kasasahen Turai su sasanta da China

Shugaban China  Xi Jinping
Shugaban China Xi Jinping REUTERS/Andrea De Silva

Kasar Jamus, ta nemi a gaggauta samar da fahintar juna tsakanin Kungiyar Tarayyar Turai da kuma China dangane da yadda kamfanonin kera motoci na kasar China za su rika biyan kudaden haraji a cikin kasashen na Turai.

Talla

Wani mai Magana da yawun ma’aikatar tattalin arziki ta kasar Jamus, ya bayyana wa manema labarai cewa, bangarorin biyu za su iya warware wannan matsala da ke tsakaninsu ne kawai ta hanyar tattaunawa.

Sai dai wasu rahotanni na cewa yanzu haka China na shirin soma karbar haraji a kan motocin da ake kerewa a Nahiyar Turai sannan kuma ake shiga da su zuwa cikin kasarta.

Masana suna ganin wannan kan iya gurgunta dangantakar kasuwanci da ke tsakanin China da kasashen Turai wanda hakan barazana ce ga kokarin da kasashen ke yin a farfado da komadar tattalin arzikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI