Rasha-Amurka

Rasha tace tana iya ba Snowden mafaka wanda ya yi layar zana bayan ya tona asirin Amurka

Edward Snowden,  wanda ya fallasa bayanan sirrin Amurka
Edward Snowden, wanda ya fallasa bayanan sirrin Amurka REUTERS/Courtesy of The Guardian/Glenn Greenwald/Laura Poitras

Gwamnatin kasar Rasha tace tana iya ba Edward Snowden mafaka wanda ya bayyana sirrin Amurka na bin diddigi wajen sauraren zantukan dubban wayoyin salular jama’a da sakonninsu na Email da sauran bayanai da suka shafe su a hanyoyin sadarwa a Intanet, Kamar yadda kakakin shugaba Vladimir Putin ya shaidawa wata Jaridar Rasha.

Talla

Jaridar Kommersant daily tace Dmitry Peskov, kakakin Shugaba Putin yace suna iya ba Snowden mafaka idan har ya nema.

Yanzu haka dai rahotanni sun ce Edward Snowden da ake zargi ya fice daga otel din da ya ke zama a Hong Kong bayan hukumomin Amurka sun bukaci a mika shi domin fuskantar bincike.

Gwamnatin Birtaniya ta mayar da martani game da alakarta da tono bayanan sirrin na Amurka bayan Snowden ya aikawa jaridar Guardian ta Birtaniya da kuma Washington Post ta Amurka da bayanan sirrin domin wallafawa.

Sakatare harakokin wajen Birtaniya William Hague ya jaddada cewar jami’an leken asirinsu ba su keta dokokin da suka takaita shiga hurumin sirrin rayuwar mutane, yana mai yin watsi da zargin bayan alakanta hukumar leken asiri ta GCHQ ta hada kawance da Amurka domin samun bayanan da suka sabawa dokokin Ingila.

“Ina son in tabbatar da cewa wannan zargi ne da baya da makama”. In ji Sakatren harakokin wajen Birtaniya William Hague.

Mista Hague yace suna daukar matakan kare sirrin mutane tare da kare tsaron Birtaniya, lamarin da yace ya taimaka wajen dakile ta’addanci a kasar.

A nasa bangaren Firaministan Birtaniya David Cameron yace ya yi imanin jami’an laken asirin Birtaniya suna aiki ne ba tare keta dokokin kasa ba.

Snowden wanda tuni ya gudu zuwa Hong kong yace ya mika bayanan sirrin ne don ya sanar da al’umma aikin da ake yi akansu tare da sanar da su ana yin aikin da ya saba masu.

Tuni dai matashin ya shaidawa wani wakilin Guardian cewa ya san aikinsa ya kawo karshe bayan aikawa da sakwannin sirrin.

Yanzu haka kuma hukumomin Amurka sun kaddamar da bincike akan Edward Snowden.

Masana dai suna ganin wannan tonon asirin alamu ne da ke nuna baraka wajen dogaro da kamfanonin leken asiri masu zaman kansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.