Amurka-Lebanon

Amurka ta kafa wa wasu ‘Yan Lebanon takunkumi saboda alakarsu da Hezbollah

Kasar Amurka ta kakaba takunkumi akan wasu ‘Yan kasar Lebanon magoya bayan kungiyar Hezbollah su hudu, bayan zarginsu da kokarin fadada ayyukan kungiyar a Yammacin Afrika.

Shugaban kungiyar Hezbollah Sayyed Hassan Nasrallah
Shugaban kungiyar Hezbollah Sayyed Hassan Nasrallah REUTERS/Sharif Karim
Talla

Amurka ta bayyana sunayen mutane daAli Ibrahim al watfa da Abbas Fawaz da Ali Ahmed Chehade da kuma Hicham Nmer, wadanda aka zarga fadada ayyukan kungiyar Hezbollah a kasashen Sierra Leone da Senegal da Cote d’Ivoire da kuma Gambia.

An zargi mutanen suna dibar matasa domin shiga kungiyar da horar da su tare da yada manufar kungiyar Hezbollah.

Takunkuman da aka kakaba musu, sun hada da rufe asusunsu da ke Amurka tare da haramta wa Amurkawa yin huldar kasuwanci da su.

Kasar Amurka dai ta dauki kungiyar ta Hezbollah a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda, a kuma cewar Sakataren ofishin baitulmalin kasar ta Amurka, David Cohen, za su yi duk iya bakin kokarinsu, suga cewa ayyukan kungiyar bai ketara iyakokin kasar Lebanon ba, inda daga nan ne kungiyar ta samo asali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI