ILO

Yara Miliyan 10 ke aikin bauta a Duniya

Wani yaro dauke da kwandon Ciyayi
Wani yaro dauke da kwandon Ciyayi DR

Kungiyar Kwadago ta duniya (ILO), tace kananan yara sama da miliyan 10 ke aiki a matsayin baran gida ko kuma masu hidima a kasashen duniya, wanda ake danganta shi da bauta. Kididigar da hukumar ta bayar, a ranar yaki da bautar ta Majalisar Dinkin Duniya, tace cikin adadin, kashi uku bisa hudu daga cikinsu, ‘Yan mata ne.

Talla

An bayyana sama da miliyan shida da rabi daga cikin ‘Yan matan de aikin bauta, shekarun su ba su wuce shekara biyar ba zuwa Goma sha Hudu ba.

Kungiyar tace matsalar na da girma a duniya, sai dai kuma tafi kamari a kasashen Burkina Faso da Ghana da Cote d’Ivoire da Mali.

Rahotan kungiyar ya koka kan yadda ake tura kananan ‘Yan mata daga Habasha zuwa Gabas ta tsakiya don aikin bauta a gidaje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.