Syria

Amirka Ta Ce Syria Na Amfani da Makami Mai Guba

Shugaban Siriya Bashar al Assad da ake zargi da amfani da makamai masu guba
Shugaban Siriya Bashar al Assad da ake zargi da amfani da makamai masu guba rfi

Hukumar Leken Asiri ta kasar Amurka wato CIA, ta ce a halin yanzu tana da cikakkun hujjojin da ke tabbatar da cewa an yi amfani da makamai masu guba a yakin kasar Syria. A taron manema labaran da ya gabatar a cikin daren jiya, kakakin fadar shugaban Amurka,  Ben Rhodes, ya ce akalla mutane 100 zuwa 150 ne suka rasa rayukansu sakamakon yin amfani da wadannan makamai a kasar ta Syria.Mai magana da yawun fadar ta White House, ya ce bangaren shugaba Bashar Assad na da hannun wajen yin amfani da wadannan makamai.