Iran

Rohani yana fatar inganta huldar Iran da kasashen Duniya

Sabon Zababben shugaban Iran Hassan Rohani yana zantawa da manema labarai
Sabon Zababben shugaban Iran Hassan Rohani yana zantawa da manema labarai Reuters/Fars News/Seyed Hassan Mousavi

Sabon Zababben shugaban kasar Iran Hassan Rohani ya bayyana fatarsa na cim ma daidaito da kasashen duniya game da shirin Nukiliyarsu, yana mai godewa al’ummar Iraniyawa da suka ba ma su sassaucin ra’ayi kuri’unsu.

Talla

A jawabinsa na farko da ‘Yan jarida, Malam Rohani yace gwamnatin shi za ta kokarin inganta huldar Iran da kasashen duniya.

A ranar Assabar ne aka bayyana sunan Rohani a matsayin sabon shugaban kasar Iran, wanda hakan zai kawo karshen mulkin Mahmoud Ahmedinejad mai ra’ayin rikau.

Sai dai kuma Rohani ya bayyana rashin gamsuwa akan takunkumin da aka kakabawa kasar Iran saboda shirinta na Nukiliya, lamarin da ya kira “rashin adalci”.

Zaben Rohani a matsayin shugaban Iran, wani kwarin guiwa ne na warware tankiyar da ke tsakanin kasar Iran da kasashen Yammaci.

Hassan Rohani ya yi gargadin adawa da matakin kasashen Turai na shiga tsakanin rikicin Syria inda ya jaddada cewa mutanen Syria ne ya dace su sasanta kansu.

Hakan dai ke nuna Gwamnatin Rohani ba zata sabawa kawance da ke tsakanin Iran da Syria ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI