Brazil

Matasa suna zanga-zanga a kasar Brazil

Masu zanga-zangar adawa da wasannin gasar cin kofin zakarun Nahiyoyin duniya da ake gudanarwa a Brazil
Masu zanga-zangar adawa da wasannin gasar cin kofin zakarun Nahiyoyin duniya da ake gudanarwa a Brazil REUTERS/Ueslei Marcelino

Akwai zanga-zanga da daruruwan matasa ke gudanarwa a kasar Brazil wadanda ke adawa da makudan kudaden da aka kashe a wasannin gasar cin kofin zakarun Nahiyoyin duniya da kuma tsadar kudaden hawa motocin sufuri.

Talla

Zanga-zangar da aka bayyana mafi girma a Brazil tsawon shekaru 20, amma ana gudanar da ita ne cikin lumana, sai dai kuma an samu arangama tsakanin ‘Yan sanda da masu zanga-zangar a birnin Rio.

Rahotanni sun ce ‘Yan sanda sun yi amfani da harsashen roba da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar.

Wasu masu zanga-zangar dai sun yi kiran lalle sai shugabar Brazil Dilma Rousseff ta yi murabus, musamman saboda adawa da babbancin da ke tsakanin attajirai da talakawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI