Rasha da Turkiya sun yi zargin Amurka da Birtaniya sun sa masu ido a taron G8
Wallafawa ranar:
Kasashen Rasha da Turkiya da Afrika ta Kudu sun bayyana bacin ransu game da yadda jami’an leken asirin Birtaniya da Amurka suka sa wa wakilan kasashe ido a taron G8 da aka gudanar a Birnin London.
wannan zargin da ake wa Birtaniya da Amurka ya fito ne daga bayanan sirrin da Edward Snowden ya yada, kuma wannan ya shafi taron kasashen G8 da aka gudanar a shekarar 2009 a birnin London.
Gwamnatin Turkiya ta bukaci bayani daga Birtaniya akan wani rahoton Jaridar guardian wanda yace jami’an leken asirin Birtniya sun sa wa Ministan kudinta ido Matuka.
A daya bangaren kuma kasar Rasha ta bayyana damuwa akan yadda Jami’an leken asirin Amurka suka kula da bayanan shugaba Dmitry Medvedev, lamarin da Rasha tace kan iya dagula huldarta da Amurka.
Firaministan Birtaniya David Cameron yace ba zai ce komi ba game da wannan batu amma bayanan da aka kwarmato abin kunya ne a dai dai lokaci da ya ke jagorantar taron kasashen G8 masu karfin tattalin arzikin duniya a Arewacin Ireland.
Bayanan sirrin sun ce tun kafin taron 2009 a London, Jami’an leken asirin Birtaniya suka yi wani tanadi na kula da sakwannin wakilan kasashen na Email da na wayoyin salula kirar Blackberry.
Haka ma wannan ne ya shafi wakilan kasashen Afrika ta kudu.
Bayanan sirrin sun ce umurnin leken asirin ya fito ne daga wani babban jami’in gwamnatin tsohon Firaminsiyan Birtaniya Gordon Brown.
Yanzu haka dai duk da wannan barakar amma Edward Snowden yace akwai dinbim bayanan sirrin Amurka da zai kwarmato a nan gaba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu