Amurka-Afghanistan

Amurka ta bukacin tautaunawa da yan Taliban

rfi

  Wani Jami’in kasar Amurkan ne, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyanawa manema labarai shirin tattaunawar tsakanin wakilan Amurka da ‘Yan kungiyar ta Taliban.Sakataren harkokin wajen kasar ta Amurka John Kerry bai ce komai game da wannan batu ba, sai dai ya yi nuni da cewa bude ofishin da ‘yan Taliban din suka yi a Doha, abu ne da suka yi marhaban da shi.Firaministan kasar Birtaniya, David Cameron, bayan kammala taron kasashen G8 da aka yi, cewa ya yi kasar ta Amurka ta yi dai dai idan har ta fara tattaunawa da ‘yan kungiyar Taliban.Kasar Amurka dai na bukatar kungiyar ta Taliban da ta kauracewa yin hulda da kungiyar Al Qaeda ne, wacce kungiya ce da ta bayyana a matsayin ‘yan ta’adda.Sai dai abin tambaya anan shine ko wannan tattaunwar za ta kawo karshen fafatawar da dakarun Amurkan ke yi da na ‘yan kungiyar ta Taliban a Afghanistan?Matakin da Hukumomin  Amurka  suka dau  na  tataunawa da  yan Taliban bai dace ba, a cewar  Aimal Faizi wani jami'in  tsaro  kasar ,sai de babu tabbacin cewar  yan Taliban za  su  yi na'am  da  tayi  hukumomin Amurka a  dai de  lokacin da  suka kashe sojan Amurka hudu  a  wani harin  da  suka  kai  a  tashar  saukar  jiragen sama  sojan Amurka  a garin Bagram.