Brazil

Arangama da dubban masu zanga zanga a Sao Paulo

Barnar da masu zanga-zanga suka yi a Sao Paulo
Barnar da masu zanga-zanga suka yi a Sao Paulo rfi

YAN Sanda a kasar Brazil sun yi arangama da dubban masu zanga zanga a Sao Paulo, matakin da ya sasu anfani da hayaki mai sa hawaye da kuma harsashin roba.Masu zanga zangar sun fasa shaguna da bankuna, inda ak asamu fito na fito tsakanin wasu masu zanga zangar da basa goyan bayan ta’adin da ake, da kuma masu aikata ta’adin.Masu zanga zangar na nuna bacin ran su dangane da tsadar farashin sufuri, da kuma makudan kudin da ake kashewa kan harkokin wasanni, sun bukaci bunkasa ilimi, makarantu da sufuri.