Brazil

An girke Jami’an tsaro domin haramta wa masu zanga-zanga shiga Filayen wasannin Brazil

Daruruwan Masu zanga-zanga a Birnin Belem, a Brazil
Daruruwan Masu zanga-zanga a Birnin Belem, a Brazil Reuters/路透社

Gwamnatin Brazil ta girke ‘Yan sanda domin kare filayen wasannin da ake gudanar da gasar cin kofin Zakarun Nahiyoyin Duniya daga masu zanga-zangar adawa da kudaden da gwamnatin kasar ta kashe saboda wasannin gasar cin kofin Duniya da kasar zata karbi bakunci a 2014.

Talla

Daruruwan mutane ne suka fito zanga-zanga a saman Titunan manyan biranen Brazil, lamarin da ya sa Shugabar Kasar Dilma Rousseff tace zata saurari koken masu zanga-zangar.

Duk da ana gudanar da zangar-zangar cikin lumana a wasu biranen amma a birnin Sao Paulo Zanga-zangar ta rikide zuwa rikici inda 'Yan sanda ke arangama da masu zanga-zangar.

Yanzu haka kuma gwamnatin kasar ta bayar da umurnin girka Jami’an tsaro a biranen da ake gudanar da gasar cin kofin Zakarun Nahoyoyin duniya na kasashe Takwas don kare lafiyar baki da kuma kwantar da tanzomar.

Masu zangar –zangar dai suna adawa ne da makudan kudaden da gwamnatin Brazil ta kashe musamman wajen gina sabbin gidaje da gyara gari domin karbar bakuncin gasar cin kofin Confederation.

Wasu kuma suna adawa ne da tsadar kudaden sufuri a kasar, lamarin da ya sa wasu ke kiran lalle sai shugabar kasar ta yi murabus.

Yanzu haka kuma rahotanni sun ce shugaba Rousseff ta gana da mai gidanta Luiz Inacio Lula da Silva domin tattauna hanyoyin kwantar da zanga-zangar.

A madadin ‘yan wasan Brazil Dan wasan Chelsea David Luiz ya bayyana nuna goyon bayansu ga masu zanga-zangar wacce za’a ce ta shafe labarin wasannin da ake gudanarwa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI