Amurka

Hukumar leken asirin Amurka ta yi nasarar magance hare haren a Amurka

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama REUTERS/Kevin Lamarque

Hukumar leken asirin Amurka, Janar Keith Alexander, yace sun yi nasarar magance hare haren ta’adanci 50 da aka shirya kai wa kasar, saboda ayyukan leken asirin da suke yi. Yayin da ya ke kare matakin sa ido da suke kan sakwannin jama’a, Alexander yace, daga shekarar 2001 zuwa yanzu, sun bankado shirin kai hare hare 50 akan muradun Amurka, a kasashen duniya 20, cikin su har da wanda aka shirya kai wa Cibiyar hada hadar kasuwancin New York.

Talla

Sai dai jami’in yace, kashi 10 daga cikin irin wadanan hare hare a gida ake shirya su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.