Amurka-Rasha

Rasha ta mayar wa Amurka da martani game da Nukiliya

Shugaban Amurka Barack Obama tare da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel  à  ziyarar da ya kai a Berlin.
Shugaban Amurka Barack Obama tare da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel à ziyarar da ya kai a Berlin. REUTERS/Thomas Peter

Mataimakin Firaministan kasar Rasha Dmitry Rogozin ya maryawa Amurka da martani game da kalaman Obama na yin aiki tare domin rage makaman nukiliya, yana mai cewa matakin baya da muhimmaci ga Rasha domin Amurka na karfafa Makamanta masu linzami.

Talla

Mista Rogozin yace laifin mallakar makamai shi ke sa kasashe su tanadi makaman.

Wannan kuma na zuwan ne bayan kiran da Shugaban Amurka Barack Obama ya yi ga Rasha a ziyarar da ya kai a kasar Jamus.

Jawabin na Shugaba Barack Obama na zuwa ne shekaru 50 a dai dai lokacin da tsohon shugaban Amurka John F Kennedy ya gabatar da jawabi a Berlin.

Shugaba Obama yace za su nemi tattaunawa da Rasha game da matakan rage makaman nukiliya karkashin wani kyakkyawan tsari na nukiliya a kasashen Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI