Majalisar Dinkin Duniya

Ana samun karuwar 'yan gudun hijira a kowace shekara a duniya

Wasu 'yan gudun hijirar Somaliya
Wasu 'yan gudun hijirar Somaliya www.amnesty.fr/‎DR

Yaki da kuma sauran bala’o’i, sun haifar da samuwar dan gudun hijira akalla daya a cikin ko wadanne kikoki 4 a shekarar da ta gabata a duniya, a cewar Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNHCR.

Talla

A rahoton da ta fitar a wannan shekara, hukumar ta ce a cikin shekaru 20 na baya bayan nan, kimanin mutane milyan 45 ne wadannan matsaloli suka tilastawa barin muhallansu ko kuma suka zama ‘yan gudun hijira a duniya.
Rahotanon ya bayar da misali da matsalolin da ake fama da su a kasashen Syria, Afghanistan da kuma Somaliya a matsayin bala’o’in da suka fi haifar da kwararrar ‘yan gudun hijira a wannan zamani.
UNHCR, ta ce a cikin shekara daya kawai, an samu ‘yan gudun hijira milyan daya da dubu dari, yayin da wasu milyan 6 da dubu dari biyar suka sami kansu a cikin yanayi na rashin muhalli ko kuma tilasta masu barin muhallansu na asali ala dole.
Antonio Gutarres, shugaban hukumar ta ‘yan gudun hijira, ya ce kusan ko wadanne kikoki hudu, akwai mutum daya daga barin muhallinsa a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI