Brazil

Mutane Miliyan Daya Suka Shiga Bore a Brazil

Masu bore a Rio de Janeiro
Masu bore a Rio de Janeiro rfi

A ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna adawa da yadda gwamnatin kasar Brazil ke kashe makuddan kudade wajen daukar nauyin kwallon kafa a daidai lokacin da talauci ke addabar jama’a, mutane akalla miliyan daya suka shiga boren. Wannan yawan mutane da suka shiga boren na zuwa ne duk da cewa Gwamnatin kasar ta yi dan sassauci game da bukatun jama’a na rage farashin shiga ababan hawa.Zanga-zangan ta kasance cikin lumana kodashike akan sami rikici a wasu manyan biranen kasar ganin yadda ake kara samun jama’a na shiga boren.A birnin Rio de Janairo inda aka sami mutane dubu dari uku na cikin boren, bayanai na cewa sai da ‘yan sanda suka rika gwabzawa da wasu dake wawushe kayan jama’a.A garin Sao Paulo an sami mutun daya daya rasa ransa, cikin masu bore a lokacin da wata mota dake sukwane ta markade shi.Magajin garin Rio de Janairo, Eduardo Paes ya fadawa taron manema labarai cewa farashin shiga ababan hawa, an rage, amma kuma masu zanga-zangan sun ce babu wani ragi da zai sa su sauya ra’ayi