Brazil

Gwamnatin Brazil ta yi nadama tare da alkawalin diba bukatun masu zanga-zanga

Dilma Roussef Shugabar kasar Brazil
Dilma Roussef Shugabar kasar Brazil AFP

Shugabar kasar Brazil da ke fuskantar suka ta yi alkawalin diba bukatun masu zanga-zanga bayan akalla mutane sama da Miliyan daya sun fito suna zanga-zangar neman a inganta rayuwarsu.

Talla

Shugaba Dilma Rousseff ta yi alkawalin yaki da cin hanci, a lokacin da ta ke jawabi ta kafar Talabijin. Wannan kuma na zuwa ne bayan kwashe kwanaki ‘Yan kasar na gudanar da zanga-zangar adawa da kudaden da aka kashe domin karbar bakuncin wasannin kwallon kafa a kasar.

Daga cikin bukatun masu zanga-zangar sun hada da inganta ilimi da kiwon lafiya tare da yaki da matsalar cin hanci da rashawa a Brazil.

“Mutane suna da ‘yancin su fito su kalubalanci gwamnati”, a cewar Rousseff.

Sai dai Russeff ta ce a matsayinta na shugabar kasar Brazil, ba za ta zura ido ana aikata barna a kan kadarorin jama’a da kuma haifar da matsaloli ga masu zirga zirga a kan titunan kasar ba.

Jawabin na shugaba Russeff ya zo ne kwana daya bayan wata babbar zanga-zangar da aka yi a kasar, inda aka ce akalla mutane Milyan daya ne suka fito domin neman a rage kudaden sufuri da kuma rage kudaden da ake kashewa wajen daukar nauyin wasanni a kasar.

Akwai dai sabanin ra’ayi da aka samu tsakanin ‘Yan wasan Brazil, inda wasu daga cikinsu suka bayyana nuna goyon bayansu ga masu zanga-zanga, daga bisani kuma kocin ‘Yan wasan, Luiz Felipe Scolari ya fito ya kare muradun gwamnati.

Zanga-zangar dai ta shafe labarin gasar cin kofin zakarun Nahiyoyin duniya da Brazil ke daukar nauyi, kuma wannan kan iya shafar gasar cin kofin Duniya da kasar zata dauki nauyi a badi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI