Amurka-Rasha-China

Amurka ta yi gargadin gurguncewar dangantaka tsakaninta da China da Rasha akan Snowden

Barack Obama da Edward Snowden wanda ya fallasa sirrin Amurka kuma wanda yanzu haka ake nema ruwa a jallo
Barack Obama da Edward Snowden wanda ya fallasa sirrin Amurka kuma wanda yanzu haka ake nema ruwa a jallo REUTERS/Bobby Yip

Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry, ya yi gargadin gurguncewar dangantaka tsakanin Amurka da Rasha da China akan ficewar Snowden da aka ruwaito ya haye jirgi daga Hong Kong zuwa Rasha bayan Amurka ta nemi a mika shi domin fuskantar hukunci.

Talla

Kerry wanda ke ziyara a kasar Indiya yace Snowden ya ci amanar kasa don haka ya dace ya fuskanci hukunci.

Tuni dai aka ruwaito Snowden zai fice daga Rasha zuwa kasar Ecuador domin neman mafaka bayan ya samu izinin ficewa daga Hong Kong zuwa Birnin Moscow a ranar Lahadi.

Sai dai kuma wata majiya ta shaidawa kamfanin Dillacin labaran Reuters cewa babu duriyar Snowden a tashar jiragen rasha don hawa jirgi zuwa Cuba. Majiyar tace kujerar da aka yi hasashen Snowden zai zauna wani fasinja ne ya haye kujerar.

Yanzu haka dai Amurka tana neman Snowden ne ruwa a jallo kuma tuni hukumomin kasar suka janye katin shedarsa na tafiye tafiye tare da kira ga sauran kasashe su haramta masa ficewa.

Snowden wanda jami’in leken asirin Amurka ne yana fuskantar tuhumar laifin fallasa sirrin kasar bayan ya mika bayanan sirri ga jaridar Guardian da Washington post.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.